United: An caccaki iyalan Glazer

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Iyalan Glazer su ne fada a ji a United

Kungiyar masu goyon bayan Manchester United ta ce matakin bai wa iyalan Glazer fan miliyan 16 a kowacce shekara bai dace ba.

Iyalan Glazer ne keda hannun jari kashi 83 cikin 100 na United, kuma ana ba su wani kaso a cikin ribar da kulob din ke samu a duk wata hudu.

"Wannan bai dace ba, kamata ya yi ribar kulob din ya kara komawa kulob din," in ji Sean Bones da ke goyon bayan United.

Mai magana da yawun kulob din ya ce iyalan Glazer sun jaddada manufarsu ta ci gaba da saka jari domin karfafa kulob din.

Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar ta Manchester United ta bayyana cewar nan gaba kadan za ta sake sayar da wani bangare na hannun jarinta.