"Babu rashin jituwa tsakani na da 'yan wasa"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho ya ce ba za a samu sauyi ba ko da ya cire Terry daga wasa.

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya musanta rade-radin da ake yi cewa ba ya jituwa da 'yan wasan kulob din, kwana guda kafin su fafata da Arsenal a Gasar Premier ta Ingila.

Kulob din shi ne na 17 a tebirin Gasar, bayan sun kasa yin katabus tun da aka fara gasar ta bana, kuma rahotanni na cewa akwai rashin jituwa tsakanin Mourinho da kyaftin din kulob din, John Terry.

Mourinho ya ce, "Babu rashin jituwa tsakani na da 'yan wasa na."

"Terry dan wasa ne nake da matukar kwarin gwiwa a kansa. Idan na bar shi a benchi, ko kuma na cire shi daga kwallo kwata-kwata, hakan ba zai sauya koma bai", in ji Mourinho.

An cire Terry daga wasa a fafatawar da kulob din Manchester City ya doke Arsenal kwana biyu da fara Gasar Premier, kuma an ba shi jan kati a wasan da suka doke West Brom.