Ya kamata FA ta binciki halayyar Costa - Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta doke Arsenal da ci 2-0 a Stamford Bridge

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce ya kamata hukmar kwallon kafa ta Ingila ta binciki dalilin da ya sa ba a bai wa Diego Costa jan kati ba a ranar Asabar.

Chelsea ce ta karbi bakuncin Arsenal a gasar Premier wasan mako na shida, ta kuma lashe karawar da ci 2-0 a Stamford Bridge.

Sai dai kuma alkalin wasan Mike Dean ya sallami mai tsaron bayan Arsenal Gabriel bayan da ya yi cacar baki da Diego Costa har ma ya taka shi a kafa.

Wenger ya ce bai ga dalilin da aka ki korar Costa daga wasan ba, duk da dukan Koscielny da ya yi a fuska.

Kocin ya ce Costa zai ci gaba da nuna wannan halin a nan gaba tun da dai ba a dauki mataki a kansa ba, kuma idan dan wasa ya tanka masa ya kwana a ciki.

Sai dai kociyan Chelsea, Jose Mourinho ya ce Wenger yana jin radadin doke su 2-0 ne da suka yi da kuma kammala wasan da 'yan kwallo tara a cikin fili.