Man United ta ci Southampton a St Mary

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester ta koma matsayi na biyu a kan teburin Premier da maki 13

Southampton ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 3-2 a gasar Premier wasan mako na shida da suka kara a St Mary ranar Lahadi.

Southampton ce ta fara zura kwallo a ragar United ta hannun Graziano Pelle, kuma shi ne ya ci ta biyu saura minti hudu a tashi daga wasan.

United kuwa ta ci kwallayenta biyu ta hannun sabon dan wasan da ta sayo Anthony Martial kan kudi £36m a bana a minti na 34 da kuma minti na 50 da ake fafatawa.

Juan Mata ne ya ci wa United kwallo ta uku da hakan ya sa ta hada maki uku a karawar ta kuma koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 13.

Southampton kuwa tana matsayi na 16 a kan teburin da maki shida bayan buga gasar wasannin mako na 6 da ta yi.