Za mu inganta damben gargajiya - Abdullahi

Image caption Wasannin gargajiya guda biyar ne da suka yi fice a Nigeria

Shugaban wasannin gargajiya na Nigeria Muhammad Baba Abdullahi ya ce za'a inganta wasannin gargajiya ciki har da damben da langa da ayo da abula.

Abdullahi ya ce Nigeria ta yi suna a wasan kokawar gargajiya a Afirka da duniya, yanzu kuma lokaci ya yi da za su saka kaimi a wasan damben gargajiya.

Ya kuma ce tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen gabatar da wasan a cikin gasar wasannin Afirka domin ciyar da wasan gaba.

Shugaban ya kuma ce sauran wasannin gargajiya da suka hada da langa da Abula da Ayo suma da akwai tsarin da suke son yi domin bunkasa su a duniya.

Ya kuma yi kira da masu ruwa da tsaki a wasannin gargajiya da su bayar da gudunmawar da za ta taimaka domin ciyar da wasannin al'adun gargajiyar Nigeria a duniya.