Damben Bahagon Sisko da Inda babu kisa

Image caption Damben da suka taka ya kayatar sai dai babu kisa a wasan

Damben da aka yi tsakanin Bahagon Sisko daga Kudu da Inda Dan Nufawa daga Arewa a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria babu kisa.

Karawar da suka yi da safiyar Lahadi sun yi turmi uku kuma wasan ya kayatar da 'yan kallo har suka yi wa 'yan wasan kyaututtuka mai yawa.

Tun farko an fara ne da sa zare tsakanin Autan Faya daga Kudu da Kura Dogon Kwalle, kuma turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa a wasan.

An yi gumurzu a karawar da aka yi tsakanin Sani Shagon Kwarkwada daga Kudu da Shagon Dogon Sani daga Arewa, kuma sau biyu suna yin amarya amma wasan babu kisa.

Damben Bahagon Sarka daga Kudu da Figot daga Arewa turmi biyu suka dambata alkalin wasa Sarkin Gida na Jafaru Kura ya raba fafatawar.

Sa zare da aka yi tsakanin Bahagon Sani Mai Maciji daga Kudu da Sojan Kyallu daga Arewa turmi biyu suka dambata shi ma babu kisa

Karawar da aka yi tsakanin Shagon Bahagon Sarka daga Kudu a karo na biyu da Abban Na Bacirawa an biya 'yan kallo an kuma yi raha sai dai babu wanda ya yi nasara a wasan

Daga nan ne aka rufe da damben Ashiru Horo daga Arewa da Mai Caji daga Kudu kuma turmi daya kacal suka taka, watakila da yammaci su sake karawa.