Kurt Zouma ya yi amai ya lashe

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Chelsea ce ta doke Arsenal da ci 2-0 a ranar Asabar a gasar Premier

Mai tsaron bayan Chelsea, Kurt Zouma ya nemi afuwa kan jawabin da ya yi cewar Diego Costa na yin kwange a wasansa.

Zouma mai shekaru 20, ya yi jawabin ne bayan da aka tashi wasan Premier da Chelsea ta doke Arsenal 2-0 a Stamford Bridge ranar Asabar.

Diego Costa ya mari Laurent Koscielny, sannan alkalin wasa Mike Dean ya kori Gabriel daga wasan bayan da ya yi cacar baki da Costa har ma ya taka shi a kafa.

Zouma ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi, ya kuma ce Ingilishi ba yarensa ba ne, saboda haka ba a fahimci kalaman nasa ba, bai kuma yi niyyar zargin kowa da kwange a wasa ba.

Ya kuma ce Costa dan kwallo ne da yake matsawa abokin karawa matsi, yana kuma mutunta shi sosai.