'Za mu kalubalanci lashe kofin Premier bana'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester United tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Doke Southampton da Manchester United ta yi, ya ba ta karfin gwiwar sa ran lashe kofin Premier bana in ji Louis van Gaal.

United ce ta ci Southampton 3-2 a filin wasa na St Mary a gasar Premier wasan mako na shida da suka kara a ranar Lahadi.

Nasarar da United ta samu ya sa ta koma mataki na biyu a kan teburin Premier da maki 13, biye da Manchester City wacce ke matsayi na daya a teburin da maki 15.

Van Gaal ya ce "Na fada a baya cewar za mu iya lashe kofin Premier, kuma da wuya ka dauki kofi lokacin da kake bunkasa 'yan wasanka, amma dab muke da fara daukar kofuna".

Haka kuma kociyan ya yaba da kwazon Anthony Martial sabon dan kwallon da ya sayo a bana daga Monaco, kan kwallaye biyun da ya zura a fafatawar.