World Cup 2010: Bincike kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Afirka ta Kudu ce ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2010

Babbar jam'iyyar hamayya ta Afirka ta Kudu ta bukaci da a gudanar da bincike kan zargin cin hanci a kan jami'ai biyu kan karbar bakuncin gasar kofin duniya a 2010.

Jam'iyyar na son a yi bincike a kan Danny Jordaan da kuma Molefi Oliphant wadanda suka jagoranci neman karbar bakuncin wasannin.

Tun farko an yi zargin cewar an bayar da cin hancin kudi da ya kai $10m domin a bai wa Afirka ta Kudu damar karbar wasannin cin kofin duniya a karon farko a Afirka.

Kasar Afirka ta Kudu da kuma hukumar wasan kwallon kafar kasar sun karyata cewar sun bayar da cin hanci.

Sai dai sun amince cewar sun bayar da kudi, amma domin a bunkasa kwallon kafa ne a Trinidad.