Dan Mahautan Kubuwa ya dambata da Autan Faya

Image caption Ashiru Horo da Mai Caji, wannan takawar da suka yi babu kisa a ranar Lahadi da safe

Garkuwan mahautan Kubuwa a karon farko ya fara dambatawa da Autan faya a wasan damben gargajiya a ranar Lahadi da yammaci.

Autan Faya daga Kudu shi ne ya nemi Garkuwan Mahautan Kubuwa da su dambata a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Sun kuma fafata har tsawon turmi uku, kuma daf da za a raba wasan Autan Faya ya samu dama ya dinga naushin Dan Mahauta amma ko gizo bai yi ba.

Daga nan ne aka sa zare tsakanin Sojan Kyallu daga Arewa da Bahagon Sani Mai Maciji daga Kudu, a inda suka yi turmi uku babu kisa aka raba damben.

Karawar da aka yi tsakanin Garkuwan Mai Caji daga Kudu da Abban Na-Bacirawa daga Arewa turmi uku suka yi, alkalin wasa Sarkin gida na Jafara Kura ne ya raba wasan.

Daga karshe ne aka rufe da wasa tsakanin Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Abata Mai kuma turmi daya kacal suka taka aka tashi daga filin wasa.