Ban yanke kauna da buga wa Chelsea ba - Atsu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Atsu ya koma Chelsea ne a shekarar 2013

Dan kwallon Ghana, Christian Atsu, ya ce ya kagara ya fara buga wa Bournemouth wasa domin ya haskaka wanda hakan zai iya ba shi damar yi wa Chelsea kwallo.

Atsu mai shekara 23, bai buga wa Bournemouth gasar Premier a kakar wasan bana ba, tun komawarsa kulob din aro daga Chelsea a 2013.

Dan wasan ya ce ya dade yana mafarkin ya buga wa Chelsea kwallo, kuma mafarkinsa zai zama gaskiya idan ya taka rawar gani a Bournemouth.

Tun lokacin da Chelsea ta dauki Atsu a Satumbar 2013, ta bayar da shi aro ga Vitesse Arnhem da Everton wacce ya buga wa wasannin gasar Premier biyar.