Ingila za ta rasa gurbi daya a gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashen Ingila ba su taka rawar gani ba a gasar zakarun Turai a shekaru biyu a jere

Ingila tana daf da rasa gurbi daya daga cikin hudun da take da su a gasar cin kofin zakarun Turai a 2017-18, idan ta ci gaba da kasa taka rawa a gasar.

Kungiyoyin Ingila sun kasa kaiwa wasan daf da na kusa da karshe a shekaru biyu a jere a gasar wasannin.

Ma'aunin da ake auna kwazon kasashe a fagen tamaula da aka yi a shekaru biyar ya nuna cewar Ingila tana mataki na uku, biye da Spaniya a mataki na daya sai Jamus ta biyu.

Italiya ce a matsayi na hudu, kuma kasashe ukun farko ne ake baiwa gurbin kungiyoyi hudu da suke buga gasar cin kofin zakarun Turai.