Navas ya yi takaicin rashin komawa Man United

Image caption Wasanni 11 Navas ya yi wa Real Madrid

Mai tsaron ragar Real Madrid, Keylor Navas, ya yi takaicin rashin komawa Manchester United a lokacin da ake cin kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo.

United ce ta bukaci ta sayar wa da Real Madrid David De Gea ita kuma a hada mata da Keylor Navas.

Sai dai kungiyoyin biyu sun gamu da tsaikon rattaba hannu a kan yarje-jeniyar, lamarin da ya hana Musayar 'yan wasan a ranar 31 ga watan Agusta.

Navas ya ce "Na yi kuka dana fahimce musayar ba za ta yiwu ba, domin na saka rai tun farko, duk da dai bana son barin Madrid".

Golan ya koma Real Madrid ne daga Levante a 2014, bayan da ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil, sai dai wasanni 11 ya buga wa Madrid.