Na so a kara min albashi - Ferguson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ferguson ya dauki kofunan Premier 13 a Manchester United

Tsohon kociyan Manchester United, Sir, Alex Ferguson ya bukaci a ninka albashinsa fiye da wanda aka kara wa Wayne Rooney a 2010.

United ta karawa Rooney albashin da yake karbar £250,000 a duk mako, bayan da ya yi barazanar barin kungiyar.

Ferguson ya rubuta a sabon littifin da ya fitar cewar ya sanar da United cewar ba a yi masa adalci ba da albashin Rooney ya rubanya nasa sau biyu.

David Moyes ne ya maye gurbin Ferguson wanda ya jagoranci United ta lashe kofunan zakarun Turai biyu da Premier 13 da FA biyar da kuma League Cups hudu.

Ferguson ya fada a littafin nasa cewar ya so ya tattauna da Pep Guardiola domin maye gurbinsa a United kafin a nada David Moyes.

Ya kuma bayyana yadda United ta auna kocin da zai ja ragamar kungiyar a gaba tsakanin kocin Chelsea Jose Mourinho da Carlo Ancelotti da Jurgen Klopp da kuma Louis van Gaal.