Mourinho ya yi Wenger hannunka mai sanda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wenger da Mourinho ba sa ga maciji

Kocin Chelsea Jose Mourinho bisa dukkan alamu ya yi wa takwaransa na Arsenal, Arsene Wenger, shagube inda ya bayyana shi a matsayin "Sarki" wanda ba ya fuskantar "matsin lamba".

Mourinho wanda bai ambaci sunan kowa ba, ya ce "Yana tsokaci a kan alkalan wasa, ya ture mutane amma babu abin da ya same shi."

Manajojin biyu sun dade suna hammaya, inda Mourinho ya kira Wenger "kwararre wajen rashin nasara".

"A wannan kasar Manaja daya ne kawai ba ya cikin matsin lamba, amma duk sauran suna cikin matsin lamba," in ji Mourinho.

Da aka tambaye shi, wa yake nufi, sai Mourinho ya ce :"Kun san shi."