An haramta wa Gabriel buga wasa daya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta samu nasara a kan Arsenal da ci 2-0 a Stamford Bridge

Hukumar kwallon kafar Ingila ta haramta wa da Gabriel buga wasa daya, sannan kuma ta ci shi tarar fam 10,000.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne bayan da ta samu dan wasan da nuna halin rashin da'a a karawar da Arsenal ta yi da Chelsea a gasar Premier.

Alkalin wasa Mike Dean ne ya kori Gabriel saboda rashin da'a da ya aikata tsakaninsa da Diego Costa a wasan da Chelsea ta samu nasara da ci 2-0.

Arsenal ce ta daukaka kara saboda dakatar da Gabriel daga buga wasanni uku tun farko da hukumar ta yanke masa hukunci.

Cikin tuhume-tuhumen da hukumar FA ta yi wa dan wasan har da kin barin fili a kan lokaci, bayan da alkalin wasa ya ba shi jan kati.

Haka kuma hukumar ta dakatar da Costa daga buga wasanni uku, saboda samunsa da laifin ta da yamutsi tsakaninsa da Laurent Koscielny.