Manchester United ta doke Sunderland 3-0

Hakkin mallakar hoto pa
Image caption United ta dare matsayi na daya a kan teburin Premier a karon farko a bana

Manchester United ta samu nasara a kan Sunderland da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na bakwai da suka kara a Old Trafford ranar Asabar.

United din ta fara cin kwallon ta hannun Depay, sannan Wayne Rooney ya ci ta biyu, bayan da ya yi wasanni 11 bai zura kwallo a raga ba.

Daf da za'a tashi daga karawar ne Juan Mata ya ci wa United kwallo ta uku da hakan ya ba ta damar hada maki uku a fafatawar.

Da wannan sakamakon United ta dare mataki na daya a kan teburin Premier da maki 16, bayan buga wasanni bakwai.

Sunderland kuwa tana matsayi na karshe na 20 a teburin da maki biyu kacal, za kuma ta buga wasan gaba da West Ham.