Damben Sarka da Bahagon Musa ba kisa

Image caption Shagon Sarka da Shagon Bahagon Musan Kaduna, babu kisa a wannan takawar

Karawar da aka yi a wasan damben gargajiya tsakanin Shagon Sarka da Shagon Bahagon Musa babu wanda ya yi nasara.

'Yan damben sun kara ne a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria ranar Juma'a da yammaci.

Bahagon Sarka dan damben kudu da Shagon Bahagon Musa daga Arewa sun yi wasan ne har turmi uku a tsakaninsu.

Shi kuwa Bahagon Soja daga Arewa kashe Ummati daga Kudu ya yi a turmin farko da suka taka.

Karawa tsakanin Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Jafaru Kura turmi daya suka taka babu kuma kisa a tsakaninsu.

Damben Dada Isa daga Arewa da Shagon Dogon Shahada daga Kudu turmi uku suka yi aka raba wasan.

Daga karshe aka rufe da wasa tsakanin Shagon Audu Na Mai Kashi daga Kudu da Bahagon Soja daga Arewa kuma babu wanda ya samu nasara a damben.