Horo da Shagon Alabo sun buga dambe

Image caption Horo da Shagon Alabo, wannan takawar babu kisa a tsakaninsu

Ashiru Horo ya dambata da Shagon Alabo a wasan damben gargajiya a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria, da yammacin Lahadi.

Tun da sanyin safiyar Lahadi ne Shagon Alabo ya bukaci su dambata a tsakaninsu, amma Ashiru Horo ya ce ba zai yi wasan ba.

Makadin 'yan dambe Mamuda Kanoma ya yi wa Horo kida da waka, ya kuma wasa Shagon Alabo, duk dai domin 'yan kallo su kalli damben.

Horo ya ce ya ki yin damben ne domin baya son ya doki mutun da safe da yammaci dan wasa ya ki fito wa, shi kuwa Shagon Alabo cewa ya yi domin ya buge Horo ya zo Abuja dambe.

Da yammacin Lahadi 'yan damben biyu sun yi wasa a tsakaninsu, kuma turmi biyu suka yi babu kisa aka raba wasan.

Bayan wasan Horo ya ce lallai jikin Shagon Alabo ya gaya masa, shi kuwa Shagon Alabo ya ce zai ci gaba da zama a Abuja har sai ya buge Horo.