Mun zaku tun kafin wasa da Aston Villa - Rodgers

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki 11

Kociyan Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce kungiyar ta kagara tun kafin ta buga wasan da ta doke Aston Villa da ci 3-2 a gasar Premier a Anfield ranar Asabar.

Rodgers ya ce ya sha fama da matsi saboda kasa samun nasara a wasanni shida baya da suka buga.

Kocin ya sanar da BBC cewar "Akwai zakuwar son lashe wasa a kungiyar, kuma karawa biyu aka doke mu, kasa da yadda aka ci Manchester City ko Chelsea ko kuma Arsenal".

Ya kuma kara da cewar "Muna kokari tukuru yayin da muke hada 'yan wasa da suke taka mana leda, muna kuma da fitattun 'yan kwallo da za su dawo buga mana wasanni".

Rodgers ya kuma ce 'yan wasansa suna iya kokarinsu matuka, kuma yana alfahari da su domin suna mayar da hankalinsu yadda ya kamata.

Kociyan ya ce akwai wasu mutane da ba sa kaunar aikin da yake gudanarwa a Liverpool, amma ya tashi tsaye tare da 'yan wasansa da yin aiki tukuru domin kai kungiyar gaba.