Enyimba ta ci Wikki Tourist 2-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sauran wasanni bakwai a kammala gasar bana

Enyimba International ta ci Wikki Tourist 2-0 a gasar Premier wasan mako na 31 da suka yi a Aba ranar Lahadi.

Da wannan sakamakon Enyimba tana nan a matakinta na daya a kan teburin Premier da maki 58, ta kuma bai wa Sunshine Stars wacce ke matsayi na biyu tazarar maki biyar.

Sauran sakamakon wasannin da aka fafata, FC Taraba da El-Kanemi Warriors tashi wasa suka yi kunnen doki, haka wasan Pillars da Warri Wolves suka buga 1-1.

Sharks kuwa doke Dolphins ta yi da ci daya mai ban haushi, Lobi da Shooting Stars suka buga canjaras, Ifeanyiubah da Giwa FC suka tashi 1-1.

Ga sakamakon wasannin mako na 31 da aka yi:

  • FC Ifeanyiubah 1-1 Giwa FC
  • FC Taraba 1-1 El-Kanemi
  • Enyimba 2-0 Wikki
  • Lobi 0-0 Shooting Stars
  • Rangers 2-1 Kwara Utd
  • Sunshine Stars 1-0 Abia Warriors
  • Kano Pillars 1-1 Wolves
  • Sharks 1-0 Dolphins
  • Akwa Utd 2-0 Nasarawa Utd