Sidiki ya zama shugaban kwallon kafar Kamaru

Image caption An gudanar da zaben ne a Yaounde a gaban jami'an Fifa

Tombi A Roko Sidiki ya lashe zaben shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru wato Fecafoot.

Sidiki tsohon sakatare janar na hukumar ya lashe zaben ne da kuri'u 59, yayin da Atah Robert Behazah ya samu kuri'u biyu kacal.

Zaben da aka gudanar a Yaounde an yi shi ne da sa idanun wakilan Fifa Primo Corvaro da kuma Prosper Abega.

A baya dai hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta tsayar da ranar Litinin domin dakatar da Kamaru daga shiga harkokin kwallon kafa idan ba ta gudanar da zaben ba.

Tun a cikin watan Yunin 2013 Fifa da hukumar kwallon kafa ta Afirka suka kafa kwamitin da ya jagoranci harkokin kwallon kafar Kamaru domin gudanar da zaben da aka yi.

An kuma kafa kwamitin ne bayan da hukumar kwallon kafar Kamaru ta soke sake zabar Iya Mohammed a matsayin sabon shugabanta, saboda zaman kaso da yake yi kafin a yanke masa hukunci kan tuhamar da ake yi masa.

A farkon watannan ne aka yanke wa Mohammed zaman wakafi na shekaru 15, bayan da aka same shi da laifin aikata ba dai-dai ba a kamfanin yin auduga na kasa Sodecoton da kotu ta yi.