Baldini da Tottenham sun raba gari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Baldini zai komaharkokin da ba na wasan kwallon kafa ba

Tottenham ta raba gari da daraktan tsare-tsarenta Franco Baldini, bayan da suka amince da soke kwantaragin dake tsakaninsu.

Baldini mai shekaru 54 ya koma Tottenham ne daga Roma a yulin 2013 a matsayin mai kula da saye da sayar da 'yan wasan kungiyar.

Tottenham ta ce Baldini ya bar kungiyar zai kuma ci gaba da harkokin da ba su shafi kwallon kafa ba.

Baldini ya yi mataimakin kociyan Fabio Capello a lokacin da ya jagoranci horas da Ingila.