Gasar Premier Nigeria za ta yi fice - Dikko

Image caption Saura wasanni bakwai a kammala gasar Premier Nigeria ta bana

Gasar cin kofin Premier Nigeria za ta yi fice nan da kankanin lokaci mai zuwa in ji shugaban gudanar da gasar Shehu Dikko.

Dikko wanda shi ne mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Nigeria na biyu ya ce an samu gagarumin cigaba a yadda ake gudanar da wasannin bana.

Ya kara da cewar kungiyoyi sukan ci wasanni a waje ba tare da an yi wata hatsaniya ba, haka kuma har yanzu babu tabbacin kungiyar da za ta lashe kofin bana duk da saura wasanni bakwai a kammala gasar.

Dikko ya kuma ce magoya bayan kungiyoyi da dama suna zuwa filaye domin kallon wasannin Premier, kuma suna yarda da kaddara ko da an doke su a wasa.

Daga karshe ya ce suna iya kokarinsu domin kara jawo masu saka hannun jari da kamfanoni domin su dauki nauyin kungiyoyin da kuma tallata gasar a duniya.

A ranar Lahadi aka buga gasar mako na 31, kuma saura wasanni bakwai kenan a kammala gasar ta bana, inda Enyimba take kan gaba a teburin gasar.