Warner ya gamu da fushin FIFA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amurka na son tisa keyar Warner daga Trinidad and Tobago

An haramta wa tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa Jack Warner shiga harkokin kwallon kafa har tsawon rayuwarsa.

Kwamitin da'a na Fifa, ya ce Mr Warner na da hannu a wata badakala da ta shafi kudi.

Matakin da aka dauka a kan Warner ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da tsarin da aka bi wajen bai wa Rasha da Qatar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya na shekarun 2018 da kuma 2022.

A shekara ta 2011 ne, Mr Warner ya yi murabus a matsayin mataimakin shugaban hukumar Fifa bayan da aka soma zarginsa da hannu a cuwa-cuwa.

A yanzu haka dai hukumomi a Amurka suna binciken Mr Warner bisa zargin hallata kudaden haramun.