CAF ta dakatar da kociyan Guinea-Bissau

Image caption CAF ta ce Torress ya yi amfani da kalaman batanci.

Hukumar kula da kwallon kafar Afirka, CAF ta dakatar da kociyan Guinea-Bissau Paulo Torres daga shiga harkokin wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na 2017 bayan ya zagi rafali.

CAF ta tuhumi Torress da laifin abin da ta kira "amfani da kalaman batanci da musgunawa a kan rafalin."

Lamarin ya faru ne a lokacin wasan da Guinea-Bissau ta fafata da Zambia a watan Yuni, wanda aka tashi babu kasar da ta ci.

Torres ba zai halarci fafatawar da 'yan wasansa za su yi da Kenya a watan Maris na shekarar 2016 da kuma wasannin da za su yi da Congo da Zambia.

Kwamitin ladabatawar hukumar kuma ya ci tarar Torres $195,000.

Sai dai dakatarwar ba ta shafi hana shi halartar fafatawar da kasarsa za ta yi da Liberia a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya na 2018 ba.