An dakatar da kyaftin din Tanzania

Image caption Wannan shi ne karo na biyu da aka samu Juma da lafin rashin da'a a shekarar 2015.

Hukumar kwallon kafar Tanzania ta haramtawa kyaftin din kungiyar kwallon kafar kasar, Juma Said, buga wasanni har tsawon shekaru biyu saboda ya yi rashin da'a.

Kwamitin ladabtarwar hukumar ya ce ya sami Juma da laifin nuna wa dan wasan Azam, John Bocco, yatsa a matsayin cin zarafi, a wasan da suka yi ranar 27 ga watan Satumba a birnin Dar es Salaam.

Kazalika, an ci tarar dan wasan mai shekaru 31 $930, sannan aka mika masa sammacin gurfana a gaban kwamitin ladabtawar kungiyar.

A watan Fabrairun wannan shekarar ma, an dakatar da Juma daga buga wasanni takwas bayan an same shi da laifin rashin da'a a kan dan wasan Azam, Aggrey Morris.

Har yanzu Juma bai ce komai a kan batun ba.