'Yan wasan United sun gaji - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester United Louis Van Gaal

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce akwai gajiya tattare da 'yan wasansa da suka buga wasanni 6 a cikin kwanaki 18, bayan sun lallasa Wolfsburg da ci 2-1 a gasar zakarun Turai.

Juan Mata ne ya zura kwallo ta farko a bugun daga-kai-sai-mai tsaron gida kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Chris Smalling ya zura kwallo ta biyu a minti na 53.

A ranar Lahadi kulob din na Manchester United zai kara da Arsenal a gasar Premier.

Louis van Gaal ya ce 'yan wasansa da yawa sun gaji sosai saboda jerin wasannin da suka buga.

United ta sha kashi a wasanta na farko a rukunin B a hannun PSV Eindhoven, amma nasarar da ta samu a kan Wolfsburg ta sa dukkannin kungiyoyi hudu da ke rukunin suna da maki uku-uku bayan wasannin bibbiyu.

Sai dai duk da gajiyar da 'yan wasan United suka yi, van Gaal ya ce kulob din yana da karsashin da yake bukata na ci gaba da haskakawa.