Premier: za a yi bore kan tsadar tikiti

Image caption 'Yan kallo masu bore a kan tsadar tikiti

Wasu masu goyon bayan kungiyoyi 20 na gasar Premier da kulob 10 na gasar zakarun Turai za su yi bore a karshen mako sakamakon tsadar kudaden tikiti.

A bara, wani bincike kan farashin tikiti da BBC ta gudanar ya nuna yadda farashin tikitin gasar Premier mafi sauki ya karu da kashi 15 cikin dari tun daga 2011.

Masu boren za su bukaci a mayar da farashin tikitin wasannin da za a buga na waje Fam 20.

Hukumar kula da gasar Premier ta ce kulob kulob suna da gagarumar rawar da za su taka domin saukaka farashin tikiti ga magoya bayansu.

Wadanda suka shirya yin boren sun kuduri daga alluna ko kwalaye masu rubuce rubuce a lokacin wasannin da za a buga tsakanin Everton da Liverpool da kuma Arsenal da Manchester United.

Sai dai akwai yiwuwar wasu kungiyoyin zasu hana magoya bayansu daga allunan.