Ba na fargabar komai — Rodgers

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rodgers bai da tabbas a Liverpool

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya ce ba ya cikin damuwa game da mukaminsa bayan da kungiyar ke tafiyar hawainiya a farkon kakar wasa ta bana.

Liverpool ta samu galaba ne a wasa daya tal cikin biyar, a yayin da za ta kara da Everton a filin Goodison Park.

"A koda yaushe ina kokari daidai yadda zan iya. Kuma ba na cikin wata damuwa," in ji Rodgers.

Liverpool ce ta tara a kan tebur inda Everton ke matakin na biyara gasar.

Wasannin karshen mako a gasar Premier:

Ranar Asabar:

  • Crystal Palace V West Brom
  • Aston Villa V Stoke
  • Bournemouth V Watford
  • Man City V Newcastle
  • Norwich V Leicester
  • Sunderland V West Ham
  • Chelsea V Southampton

Ranar Lahadi:

  • Everton V Liverpool
  • Arsenal V Man Utd
  • Swansea V Tottenham