Manchester City ta lallasa Newcastle 6-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City ta hada maki 18 a gasar Premier

Manchester City ta ci Newcastle United 6-1 a gasar Premier wasan mako na takwas da suka yi a Ettihad ranar Lahadi.

Newcastle ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Mitrovic a minti na 18 da fara tamaula, kuma Aguero ya farke wa City kwallo daf da za a ta fi hutu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu ne Aguero ya zazzaga kwallaye hudu a ragar Newcastle a minti na 49 da 50 da 60 da kuma 62.

Sabon dan wasan da City ta sayo a bana De Bruyne shi ma ya ci kwallo a minti na 53.

Manchester City ta hada maki 18, a inda Newcastle United har yanzu ba ta ci wasa ba a gasar Premier bana.