Southampton ta ci Chelsea 3-1 har gida

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier bana

Chelsea ta sha kashi a hannun Southampton da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na takwas da suka fafata a Stamford Bridge ranar Asabar.

Chelsea ta fara cin kwallo a raga ta hannun Willian daga bugun tazara, a inda Steven Davis ya farke wa Southampton kwallon da aka zura mata.

Sadio Mane ne ya kara ci wa Southampton kwallo ta biyu sanan Graziano Pelle ya kara cin ta uku wanda hakan ya sa ka koma mataki na tara a kan teburin Premier.

Wannan shi ne karo na hudu da Chelsea ke yin rashin nasara a gasar Premier, kuma ta koma matsayi na 16 a kan teburin Premier.