Liverpool ta sallami kociyanta Rodgers

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Liverpool tana mataki na 10 a kan teburin Premier bana

Kungiyar Liverpool ta raba gari da kociyanta Brendan Rodgers, yayin da ta sallame shi daga aikin horas da 'yan wasanta.

Liverpool wacce ta buga wasa 1-1 da Eveton a Goodison Park a gasar Premier wasan mako na takwas ya sa tana maki na 10 a kan teburin gasar cin kofin bana.

Liverpool din ce ta bayar da sanarwar korar Rodgers, ta kuma ce tana fatan nada sabon kocin da ya dace a kuma lokacin da ya kamata.

Rodgers wanda ya karbi aikin horas da Liverpool a watan Yunin 2012, ya jagoranci kungiyar kammalawa a mataki na biyu a gasar Premier ta 2013-14.

Ana hasashen cewa Liverpool za ta tuntubi Carlo Ancelotti ko Frank de Boer ko kuma Jurgen Klopp domin maye gurbin Rodgers.