Mai caji ya buge Ashiru Horo a damben gargajiya

Image caption Mai Caji ne ya buge Horo a turmi na biyu da suka taka a ranar Lahadi

Mai caji ya kashe Ashiru Horo a damben gargajiya da suka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Tun farko makadin 'yan dambe Mamuda Kanoma ne ya hada wasan, bayan da ya wasa Horo sannan ya yi wa Mai Caji kida.

Horo dan damben Arewa ya shiga filin wasa tare da Mai Caji daga Kudu, kuma nan take suka fara wasa, a inda a turmin farko babu kisa.

Ana dawo wa turmi na biyu ne suka yi Amarya suna kai wa juna duka, sai kawai ga Horo a kasa, kuma nan da nan ya mike ba tare da ya jira an daga shi ba.

Tun kafin wasan su Horo da Mai Caji an fara fafatawa tsakanin Autan Faya daga Kudu da Bahagon Na Bacirawa daga Arewa kuma turmi biyu suka yi babu kisa.

Dambatawar da aka yi tsakanin Bahagon Musan Kaduna daga Arewa da Garkuwan Autan Sikido daga Kudu shi ma babu wanda ya je kasa a turmi biyu da suka yi.

Shi ma wasan Bahagon Sisko daga Kudu da Abban Shamsu kanin Emi daga Arewa dana Fijot daga Arewa da Bahagon Sarka babu wanda ya yi nasara a karawar.