Heartland ta doke Enyimba da ci 2-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Saura wasanni shida kenan a kammala gasar firimiyar Nigeria ta bana

Heartland ta ci Enyimba 2-1 a gasar firimiyar Nigeria wasannin mako na 32 da suka kara a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Wikki Tourist ta doke Taraba FC da ci daya mai ban haushi, ita ma Nasarawa United 1-0 ta ci Lobi Stars.

Wasan Shooting Stars da Bayelsa United dana Dolphins da Ifeanyiubah da kuma na Giwa FC da Kano Pillars tashi suka yi babu ci.

Ita kuma El-Kanemi Warriors kwallaye 2-0 ta ci Sharks ta garin Fatakwal, sai kuma Akwa United ta yi rashin nasara a gidan Kwara United da ci 2-1.

Tun a ranar Asabar Abia Warriors da Enugu Rangers suka buga 3-3, Warri Wolves ta ci Sunshine Stars da ci 3-0.

Ga sakamakon wasannin mako na 32 da aka buga:

  • Dolphins 0-0 FC Ifeanyiubah
  • El-Kanemi 2-0 Sharks
  • Wikki 1-0 FC Taraba
  • Shooting Stars 0-0 Bayelsa Utd
  • Nasarawa Utd 1-0 Lobi Stars
  • Kwara Utd 2-1 Akwa Utd
  • Giwa FC 0-0 Kano Pillars
  • Heartland 2-1 Enyimba
  • Abia Warriors 3-3 Rangers
  • Wolves 3-0 Sunshine Stars