Advocaat ya ajiye aikin horas da Sunderland

Image caption Advocaat ya ce ya bar aikin ne domin Sunderland ta nemo wanda zai iya fitar da ita daga halin da take ciki

Mai horas da Sunderland, Dick Advocaat ya yi ritaya daga jagorantar kungiyar bayan da ya kasa cin wasa tun fara gasar cin kofin Premier bana.

Advocaat mai shekaru 68, dan kasar Netherlands ya karbi aikin horas da Sunderland a watan Maris, lokacin da kungiyar ke daf da faduwa daga gasar Premier bara.

Kocin ya jagoranci kungiyar ta ci gaba da zama a Premier a bara, ya kuma yi niyyar ajiye aikin a lokacin, amma ya sake tsawaita zamansa tsawon shekara daya.

Shi ma Zeljko Petrovic ya bi sahun Advocaat a inda ya ajiye aikin mataimakin mai horas da Sunderland nan take.

Tun lokacin da Sunderland ta kori Steve Bruce daga 2011, ta dauki masu horar da ita tamaula da suka hada da Martin O'Neill da Paolo di Canio da Gus Poyet da kuma Advocaat.

A ranar Asabar ce Sunderland ta buga 2-2 da Wesat Ham a gida a gasar Premier, kuma hakan ne ya sa ta yi wasanni takwas ba tare da ci wasa ba.

Hakan ne ya kuma sa kungiyar ke mataki na 19 a kan teburin Premier da maki uku kacal.