Klopp zai maye gurbin Rodgers a Liverpool

Image caption Klopp ya kai Borussia Dortmund wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai

Jurgen Klopp na sawun gaba a matasayin kociyan da zai iya maye gurbin Brendan Rodgers a Liverpool wanda aka kora a ranar Lahadi.

Liverpool ta sallami Rodgers daga aiki bayan shekaru uku da rabi da ya jagoranci kungiyar, tana kuma mataki na 10 a kan teburin Premier ta bana.

Har yanzu Liverpool ba ta kai ga cimma yarjejeniya da Klopp ba, wanda ya lashe kofunan Bundesliga biyu a Borussia Dortmund ta Jamus.

Shi ma tsohon kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti, yana daga cikin wadanda ake ganin za a iya ba aikin horas da Liverpool din.

Wasanni hudu Liverpool ta lashe daga cikin guda 12 da ta buga a bana, ciki har da wanda ta doke Carlisle a bugun fenariti a Capital One Cup.

Rodgers wanda ya karbi aikin horas da Liverpool a watan Yunin 2012, ya jagoranci kungiyar kammala gasar Premier a matsayi na biyu a 2013-14.