'Tsaka mai wuya a gasar Premier'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekaru uku da rabi Rodgers ya jagoranci Liverpool

Liverpool ta kori Brendan Rodgers daga aikin horas da kungiyar, yayin da Dick Advocaat ya yi murabus daga jagorantar Sunderland, shi kuwa Jose Mourinho ya ce sai dai Chelsea ta sallame shi daga aikin amma ba zai bar Stamford Bridge ba.

Shin me yake faruwa a gasar cin kofin Premier ne?

Me ya sa kociyoyin gasar suke shiga tsaka mai wuya duk da cewa wasanni takwas aka buga a Premier bana?

Rodgers wanda ya jagoranci Liverpool shekaru uku da rabi, shi ne mai horas da 'yan wasa na biyu gasar da ya fi dade wa.

Kimanin wata guda ba a doke Liverpool a wasa ba tun bayan da Manchester United ta buge ta ranar 12 ga watan Satumba-- amma hakan bai hana ta cin karo da koma baya ba a bana, musamman kasa lashe wasanni da kungiyoyin da ake ganin nan take za ta doke.

Nasarar da ta samu a Premier ba zai wuce doke wasanni biyu da fara gasar bana ba da kuma doke Aston Villa wacce ake ganin ita ma tana fama da matsalar rashin kokari a gasar.

'Liverpool'

Magoya bayan Liverpool musamman wadanda suka dade suna mara wa kungiyar baya, sun saba ganin fitattun 'yan wasa da masu horar da kungiyar da suka kware a kan aikinsu.

Duk da cewar Rodgers ya jagoranci kungiyar daf da lashe kofin Premier a 2013/14, iya kokarin da kocin ya yi kenan.

Wanda ake ganin zai iya maye gurbin Rodgers shi ne Jurgen Klopp, tsohon kociyan Borussia Dortmund wanda ya jagoranci kungiyar lashe gasar Bundesliga da kuma kai ta wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a 2013.

Klopp ba ya aiki tun lokacin da ya ajiye ragamar horas da Dortmund a bara. Da yake yana daga cikin fitattun masu horas da tamaula a duniya, shi ne zai fi zama kan gaba wajen zabi daga mahukuntan Liverpool koda yake ana hangen cewa tsohon kociyan Real Madrid Carlo Ancelotti zai iya aiki a Anfield idan an samu matsala da Klopp.

Sai dai kuma Klopp ya amince ya karbi aikin shi ne ba a da tabbas, kuma shi yasa Liverpool ta farga take son daukar wanda ya dace.

Akwai kuma wasu kungiyoyi da ake ganin za su iya korar masu horar da su da hakan ke nuna cewar za a samu karin wuraren aikin koyar da kungiyoyi kwallon kafa.

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Jose Mourinho'

Bayan da Southampton ta doke Chelsea a Stamford Bridge da ci 3-1, kocin Chelsea Jose Mourinho ya yi muntuna bakwai yana jawabi a kafar yada labarai a inda ya sanar da jita-jitar cewa watakila a kore shi daga aiki.

Ya kuma nace cewar ba zai yi murabus ba, amma ya san cewar zai shiga matsi.

Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier bana, kuma ta gamu da munanan sakamakon wasanni ciki har da rashin nasara a hannun Manchester City da Everton da Crystal Palace da kuma Southampton da kuma yin canjaras da Newcastle da kuma Swansea.

Wadannan sakamakon ne kashin bayan rikata-rikitar da Chelsea ta tsinci kanta a ciki.

Masu gudanar da gasar Premier suna sane cewar daga bara, za a fara biyan nuna wasannin gasar a talabijin da ya kai dala biliyan 7.8, duk kuma wasa daya da za a nuna gidan talabijin din zai kashe dala miliyan 15.5.

Saboda haka babu kungiyar da ba za ta bukacin kudin ba, shi ya sa kungiyoyin da ba fitattu bane a gasar suka fitar da kudade suka sayo 'yan wasa.

Crystal Palace ta sayo dan wasa Yohan Cabaye daga Paris Saint-Germain; Stoke City kuwa Xherdan Shaqiri ta dauko daga Inter Milan kan kudi dala miliyan 18.2; West Brom dan kasar Venezuela Salomon Rondon mai taka ledsa a Zenit St Petersburg.

Hakan kuma ya sa an samu sakamakon wasanni da suka bayar da mamaki tun kawo gasar mako na takwas, kowacce kungiya tana da damar samun maki a kan kowanne kulob.

Ita kanta Manchester City ta gamu da cikas bayan da West Ham ta doke ta gida.

Saboda haka duk da wasannin gasar ba su yi nisa ba, masu horas da kungiyoyin gasar sun fara shiga matsi, saboda babu wani shugaban da yake jagorantar kungiya da bai so karbar kabakin alherin da za a raba a gasar bara ba.

Hakkin mallakar hoto AP

'Dick Advocaat'

Tuni Advocaat ya yarda kwallon mangwaro, a inda ya ce ya bayar da isasshen lokaci ga duk wanda zai gaje shi ya farfado da Sunderland.

Yanzu haka an mayar da hankali kan kociyan Aston Villa Tim Sherwood wanda kungiyar ke mataki na 18 a kan teburin Premier da kuma Steve McClaren wanda Newcastle United ke matsayi na karshe a kan teburin.

Villa ta lashe wasan farko a Premier bana, bayan da ta doke sabuwar kungiyar da ta hau gasar Bournemouth, tun kuma daga lokacin ta kasa tabuka abin a-zo-a-gani, yayin da ta yi rashin nasara a wasanni hudu a jere, kuma sabbin 'yan wasan da ta dauko sun kasa saba wasa da tsoffin 'yan kwallon da ke kungiyar.

Ita kuwa Newcastle har yanzu ba ta lashe wasa ba karkashin Steve McClaren a gasar Premier bayan buga wasanni takwas da ta yi.

Saboda haka McClaren na fatan ya fara samun nasara a wasanni idan ba haka ba shi ne kociya na gaba da zai iya rasa aikinsa.