Al Ahly ta kori kocinta Mabrouk

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Lahadi aka fitar da Al Ahly daga gasar Confederation Cuo

Al Ahly ta sallami kociyanta Fathi Mabrouk, bayan da ta kasa lashe babban kofi a karon farko tun 2003-2004.

Al Ahly ta raba gari da Mabrouk ne, bayan da Orlando Pirates ta fitar da ita daga gasar Confederation Cup wasan daf da karshe a ranar Lahadi.

Haka kuma kungiyar ta kori daraktan wasanninta Alaa Abdel Salek daga aikinsa.

Tuni ta sanar da nada tsohon dan wasanta Abdel Aziz Abdel Shafi da aka fi sani da Zizo a matsayin kociyan rikon kwarya a karo na biyu.

Zizo ya fara jagorantar Al Ahly bayan da aka sallami Al Badry a shekarar 2010.

Mabrouk ya fara aiki da Al Ahly a watan Mayun 2014, bayan da ya maye gurbin Juan Carlos Garrido.