Babu kuskure a daukar Moyes - Ferguson

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alex Ferguson ya mara wa David Moyes baya.

Tsohon kocin Machester United, Sir Alex Ferguson ya ce ba a yi kuskure ba wurin daukar, David Moyes a matsayin wanda zai maye gurbinsa a Old Trafford.

Ferguson ya bayyana goyon bayan sa ga nadin David Moyes, wanda shi ne tsohon kocin kulob din Everton da aka kora bayan watanni takwas, a wani shiri na bayyana gaskiya da BBC za ta watsa.

"Mun yi iyakar kokarin mu, duk da halin da muka samu kan mu, " in ji Ferguson mai shekaru 73.

Ya kara da cewa,"Mun zabi wanda da ya dace."

Ferguson ya yi murabus bayan shekaru 26 a matsayin manajan Manchester United a shekara ta 2013, inda ya bayar da shawarar daukar David Moyes domin ya maye gurbin sa.

A yanzu dai Louis Van Gaal ke kocin tawagar.