Fifa na yi min zagon kasa kan takarata - Chung

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar 26 ga watan Fabrairu za a yi zaben shugaban hukumar Fifa

Chung Mong-joon ya ce kwamitin da'a na Fifa na bincikarsa, wanda hakan ya zamo zagwan kasa da ake yi masa kan takarar da yake yi.

Chung Mong-joon, yana daga cikin masu yin takarar kujerar shugabantar Fifa, domin maye gurbin Sepp Baltter a zaben da za a yi a cikin watan Fabrairu.

Dan kasar Koriya ta Kudu mai shekaru 63, ya ce an sanar da shi cewar ya karya ka'idoji shida na kundin Fifa kan da'ar ma'aikata.

Chung Mong-joon ya ce bai aikata badede ba a Fifa, kuma har yanzu hukumar ba ta ce komai ba kan ikirarin da ya yi.

Chung na daga cikin wadanda za su yi takarar shugabancin Fifa tare da Yarima Ali bin Al Hussein na Jordan da Michel Platini da kuma Musa Bility.

Sepp Blatter wanda aka zaba ya jagoranci Fifa karo na biyar, ya amince da zai yi murabus daga shugabantar hukumar, bayan zargin cin hanci da rashawa da suka mamaye ta.