An dakatar da Sepp Blatter a Fifa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Blatter na fuskantar tuhuma kan cin hanci da rashawa

Mambobin kwamitin da a na hukumar kwallon kafar duniya Fifa sun dakatar da Sepp Blatter daga shugabantar Fifa na tsawon watanni uku.

Kwamitin ya yi zama kan yanke wannan hukuncin ne bayan da gwamnatin Switzerland ta fara tuhumar Blatter kan zargin cin hanci a Fifa a watan jiya.

Ana zargin Blatter da saka hannu kan kwantiragin da ba ta shafi Fifa ba, sannan aka biya Platini wasu kude kan kwantiragin.

Blatter wanda ya fara jagorantar Fifa tun daga 1998 tare da Platini sun karyata zargin da ake yi musu.

Har yanzu kwamitin bai yanke hukuncin ko zai dakatar da Platini ko kuma akasin hakan.