An tuhumi Gascoine da tura sakonnin cin zarafi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gascoigne zai amsa gayyatar kotu a ranar 29 ga watan Oktoba

Ana tuhumar tsohon dan kwallon Ingila, Paul Gascoigne da musguna wa tsohuwar budurwarsa da aika sakonnin cin zarafi.

An tumi Gascoine mai shekaru 48, da musguna wa Amanda Thomas da aika mata sakonni ta twitter da ta wayar hannu da yawan kira a waya har mako biyu a cikin watan Maris.

Haka kuma ana zarginsa da musguna wa mai sana'ar daukar hoto Andy Stone shi ma cikin tsawon mako biyun a watan Maris din.

Gascoine zai amsa gayyatar a kotun majistare da ke Bournemouth a ranar 29 ga watan Oktoba.

Dan wasan, wanda ya taka leda a Newcastle United da Tottenham da Lazio da Rangers da Middlesbrough da kuma Everton, ya yi kaurin suna wajen shan barasa, ya kuma dauki shekaru a wajen gyaran dabi'u.