An nada Ahmed Musa kyaftin din Super Eagles

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ahmed Musa ya buga wa Super Eagles wasanni 52 ya kuma ci kwallaye 11 a raga

Kociyan Super Eagles, Sunday Oliseh ya nada Ahmed Musa a matsayin sabon kyaftin din tawagar kwallon kafar Nigeria.

Ahmed Musa wanda ke murza leda a kungiyar kwallon kafa ta CSKA Moscow ya maye gurbin Vincent Enyeama wanda ya buga wa Nigeria wasanni 101.

BBC ta fahimci cewar Oliseh ya bai wa Ahmed kyaftin ne bayan da Enyeama ya makara zuwa sansanin atisaye da ke garin Fatakwal.

Ranar Litinin Oliseh ya tsayar rana ta karshe don halartar sansanin horon a Fatakwal, amma sai a ranar Talata Enyeama ya je wurin.

Ahmed Musa wanda ya buga wa tawagar kwallon kafar Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekara 20 da kuma ta 23 ya fara yi wa Super Eagles wasa a shekarar 2010.

Nigeria za ta kara a wasan sada zumunta da Congo a ranar Alhamis, sannan ta fafata da Kamaru a ranar 11 ga watan Oktoba a Belgium.