Walcott na son gurbin mai cin kwallo a Ingila

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ingila za ta buga wasan karshe ne da Lithuania a ranar Litinin

Theo Walcott na son a ba shi matsayin mai cin kwallo a tawagar kwallon kafar Ingila, idan har Rooney ba zai iya buga wasan da za su yi da Estonia ba.

Ingila za ta karbi bakuncin Estonia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a ranar Juma'a a Wembley.

Watakila Rooney dan kwallon Manchester United ba zai buga wa Ingila karawar ba, sakamakon raunin da ya ji, bai kuma je atisaye kwanaki biyu ba.

Kocin Ingila, Roy Hodgson yana saka Walcott dan wasan Arsenal buga gefe daga gaba (Lamba bakwai) a wasannin Ingilar.

Walcott ya ce fatansa ya koma buga gurbin mai ci wa Ingila kwallaye (lamba tara) kuma abin da jama'a ke fatan su ga ya samu damar kenan.

Ingila ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci, bayan da ta ci San Marino 6-0 a ranar 5 ga watan Satumba.