West Ham ta raba gari da Amalfitano

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption West Ham tana mataki na 6 a kan teburi da maki 14

West Ham ta amince da soke kwantiragin da ta kulla da Morgan Amalfitano, saboda rigima da ya yi da kociyanta Slaven Bilic.

Amalfitano mai shekaru 30, dan kasar Faransa ya dawo taka leda West Ham ne daga Marseille a bara saboda irin wannan halin da ya aikata.

Dan wasan ya rattaba kwantiragin tsawaita zamansa a Hammers shekaru biyu da rabi a cikin watan Maris.

Amalfitano ya buga wa West Ham wasanni 28 a bara, sannan ya buga mata karawa hudu a bana ciki har da gasar Europa League.

A watan Agusta aka umarci dan kwallon ya koma wasa a karamar kungiyar West Ham, bayan hatsaniyar da ya yi da Bilic.