Fifa ta dakatar da Blatter, Valcke da Platini

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Blatter da Platini na fuskantar tuhuma

Hukumar kwallon kafar duniya Fifa ta dakatar da shugaba da Sakatarenta, wato Sepp Blatter, Jerome Valcke da Michel Platini na tsawon watanni uku.

Kazalika, hukumar ta dakatar da tsohon matamakin shugabanta, Chung Mong-joon tsawon shekaru shida, kana ta ci tarar sa £67,000.

Kwamitin kula da da'a na hukumar ne ya dauki wannan mataki.

Ana bincike kan Blatter, Valcke shugaban Uefa Platini da hannu a cin hanci da rashawa.

"Wannan matakin ya biyo bayan binciken da kwamitin da'a ya gudanar a kan mutanen," in ji sanawar Fifa.

An haramta wa mutane ukun shiga harkokin kwallon kafa na tsawon wannan lokacin. Dukkansu uku sun musanta aikata ba daidai ba.

Kwamitin da'a na Fifa ya soma bincike ne a kan Blatter bayan da babban mai shigar da kara na gwamnatin Switzerland ya soma bincike a kan Blatter mai shekaru 79.