Klopp ya zama sabon kocin Liverpool

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jurgen Klopp

Jurgen Klopp ya amince da kwantiragin zama kocin Liverpool na shekara 3.

Klopp dan kasar Jamus mai shekara 48 ya maye gurbin Brendan Rodgers wanda aka kora ranar Lahadi bayan ya shafe shekara uku da rabi a Liverpool, inda kulob din ya ke mataki na 10 a Premier.

Tun a cikin watan Mayu ne Klopp yake hutun kammala kwantiraginsa da Borussia Dortmund inda ya shafe shekaru 7 a matsayin koci.

Ana sa rai zai yi aiki tare da Zelkjo Buvac da Peter Krawietz, wadanda ya yi aiki tare da su a Dortmund, a matsayin mataimakansa a Liverpool din.

Da safiyar Juma'a ne za a gabatar da Klopp a matsayin sabon kocin na Liverpool.