Messi zai fuskanci shari'a kan haraji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lionel Messi

Wata kotu a Spain ta ce dan wasan Barcelona, Lionel Messi da mahaifinsa za su fuskanci shari'a bisa zarginsu da yin coge wajen biyan haraji.

Alkalin da ke sauraron karar ya ki amincewa da bukatar da masu shigar da kara suka yi ta a jingine tuhume tuhumen da ake yi wa dan kwallon.

Ana tuhumar Messi da mahaifinsa, Jorge ne da yin coge wajen biyan harajin da ya haura Yuro miliyan 4.

Masu shigar da kara sun yi zargin cewa Mista Jorge ya zame wa biyan haraji a kan kudaden da dansa Messi ya samu ta hanyar amfani da wasu kamfanoni na kasashen waje a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009.

Kamfanonin da mahaifin Messi ya yi amfani da su a wancan lokaci an yi musu rijista ne a Belize da Uruguay.

Lauyoyin Messi sun dage kan cewa a rayuwar dan wasan, bai taba mayar da hankali ba wajen sanin me kwantiragi da kamfanonin ta kun sa.