Sergio Aguero ya ji rauni a cinyarsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan bai dade da fara murza leda ba bayan jinyar da ya yi.

Dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ya yi rauni a cinyarsa a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da Argentina da doke Ecuador 2-0.

An fitar da Aguero daga filin wasa a minti na 22.

Dan wasan ne ya zura kwallaye biyar a wasan da City ta doke Newcastle ranar 3 ga watan Oktoba.

Za a yi wa Aguero, mai shekaru 27 a duniya, gwaje-gwaje, kuma da alama ba zai buga fafatawar da Argentina za ta yi da Paraguay a makon gobe ba.

Dan wasan bai dade da komawa filin kwallo ba, bayan jinyar da ya yi sakamakon raunin da ya yi a kwaurinsa a farkon kakar wasa ta bana.